Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Putin a Bainar Jama'a


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

A karon farko bayan da ya bace har na makonni biyu, jiya shugaba Putin ya bayyana a bainar jama'a

A Rasha karon farko kusan mako biyu shugaban kasar Vladimir Putin ya bayyana a bainar jama'a, bayan anyi kwanaki ana yada jita-jitar ko bashi da lafiya, ko ya mutu, ko kuma na hannun damansa sun yi masa juyin mulki.

Mr. Putin ya bayyana gaban 'yan jarida tareda shugaban kasar Kyrgyz Almazbek Atambayev a fadar gwamnatin da ake kira St Petersburg Konstantin, gabannin shawarwari da shugabannin biyu suka gudanar.

Mr. Atambayev yace a rage yada "jita-jita" kan shugaban na Rasha. Yace, Mr Putin ya tukasu ya gewaya dashi cikin fadar, wanda injishi ya nuna cewa ba kawai shugaban yana tafiya da karfinsa ba har ma yana gudu".

Shugaban na Rasha da murmushi yace "rayuwa ba zata yi armashi ba tareda ana yada jita-jita ta karya ba".

Ahalinda ake ciki kuma, Amurka da Jamsu sunyi alwashin zasu ci gaba da ladabatar da Rasha ta wajen amfani da takunkumi karya tattalinarzikinta saboda kama yankin Crimea, suka kuma gargadi Rasha cewa zata fuskanci karin wasu sabbin takunkumi idan Moscow bata bada cikakken hadin kai ga shirin tsagaita wuta da ta goyi bayansa ba cikin watan jiya.

Da take magana jiya a Washington, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Jen Psaki tace muddin Rasha taci gaba da mamaye yankin Crimea haka ma takunkumin da aka aza mata zasu dore.

A Berlin shugabar kasar Angela Merkel ta gana da shugaban Ukraine Petro Poroshenko wanda ya kai ziyara kasar. Daga bisani tace a shirye kungiyar tarayyar turai take tayi nazarin azawa Rasha karin takunkumi saboda goyon bayan da kasar take baiwa 'yan tawayen Ukraine a gabashin kasar.

XS
SM
MD
LG