Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama Yayiwa Wasu Fursunoni 102 Afuwa


 Barack Obama
Barack Obama

Shugaba Barack Obama na Amurka dake kamalla mulkinsa a wannan shekara, ya sake yin afuwa akan karin fursunoni 102 da aka yanke wa hukuncin dauri a bisa laifukkan da ba’a taba lafiyar wasu ba.

Wannan akidar sakin fursunonin karin wata alama ce ta kudurin shi Obama din na kokarin gyara abinda yake ganin ba’a yi cikin adalci ba, inda aka yanke wa wasu hukuncin dauri na lokacin da ya wuce gona da iri.

Da sakin wadanan 102 na baya-bayan nan, jimillar fursunonin da shugaba Obama ya sa a yi wa ahuwa, a sake su, ta kai mutane 774 ke nan, a cewar wani lauytan fadar shugaban ta White House mai suna Neil Eggleston.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG