Shugabannin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya sun tattaru don gudanar da taronsu na koli na shekara-shekara.
Kungiyar kasashen guda 7, da ake kira G-7 a takaice sun hadu a birnin Biarritz dake kasar Faransa.
Barazanar da shugaban Amurka Donald Trump yayi gabanin taron ta kara haraji akan barasar Faransa, daya daga cikin manyan kamfanonin kasar da ta karbi bakuncin taron, ta kara zafafa takaddama a tsakanin shugabannin, da har yanzu basu sami fahimtar juna ba game da batutuwan da suka shafi sauyin yanayi, da yadda za a shawo kan batun China da kuma Iran, da batun ko a maido da Rasha cikin kungiyar ko a’a, da kuma shirin ballewar Burtaniyya daga tarayyar Turai.
Da duk wadannan rarrabe-rarraben da aka samu, zai yi wuya a sami amincewar cimma matsaya. Bayan zaman farko da suka yi a yau Lahadi, shugabannin ba su iya cimma yarjejeniya akan batun sake maido da Rasha a cikin hadakar kasashen ba a shekarar 2020. An dai fidda Rasha daga kungiyar ne bayan da ta mamaye Ukraine ta kwace yankin Crimea a shekarar 2014.
Facebook Forum