Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya kai ziyara Yola da Mubi, a wani al'amarin dake nuna cewa an fara samu kyautatuwar tsaro, kuma da alama sojojin Najeriya na samun galaba a kan mayakan kungiyar Boko Haram. Idan ba a manta ba dai a 'yan watannin da suka gabata yawancin kauyukan wannan yanki su na hannun mayakan Boko Haram.
Da safiyar Alhamis din nan da misalin karfe goma sha daya jirgin saman shugaba Goodluck Jonathan ya sauka a babban filin jirgin saman jahar Adamawa dake garin Yola. Bayan saukar babban bakon a Yola, kafin ya wuce zuwa Mubi, ma'aikacin Sashen Hausa na Muryar Amurka a nan birnin Washington, DC, Ibrahim Ka'almasih Garba, ya tuntubi wakilin Sashen a jahar Adamawa Ibrahim Abdulaziz yayi bayani game da ziyarar ta bazata: