Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya isa birnin Moscow domin tattauna da takwaran aikinsa na kasar Rasha Vladimir Putin.
Ziyarar ta sa na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Turkiyya suke shirin kaddamar da wani hari akan mayakan Kurdawa na YPG da ke Siriya.
A makon da ya gabata, Erdogan ya rubata a cikin jaridar Rasha Daily Kommersant cewa, ba za su nemi shawara daga wurin kowa ba, kan yadda za su yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda, wadanda ayyukansu suka jefa al’umarmu cikin mawuyacin hali na tsawon sama da shekaru 30.
Gwamnatin Turkiyya ta dauki kungiyar YPG da jam’iyar siyasa ta YPD a matsayin ‘yan ta’adda da su ke tada kayar baya a cikin kasar Turkiyya.
Gwamnatin Turkiyya da Rasha suna goyon bayan bangarorin da ke adawa da juna ne a yakin basarar da ake yi a Siriya, lamarin da ya kai ga Turkiyya ta harbo wani jirgin yakin Rasha a shekarar 2015.
Facebook Forum