Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gurfanar Da Madugun Fasa-korin Fodar Iblis A Mexico "El-Chapo" Gaban Kuliya.


 Joaquin "El Chapo" Guzman, shine daga hanun dama.
Joaquin "El Chapo" Guzman, shine daga hanun dama.

Mexico ta tusa keyar Guzman zuwa Amurka a daren Alhamis.

Madugun safarar fodar Iblis a Mexico, Joaquin,wanda aka fi sani da "El-Chapo" yaki ya amsa laifi na tafiyarda gagarumar fasa-korin kwayoyi a yankin arewacin nahiyar Amurka, da suka hada harda halakawa da sace mutane.

Guzman,wanda yayi magana ta lauyoyinsa da kotu ta bashi,jiya Jumma'a ne a gaban wata kotun Amurka dake New York yaki ya amsa laifuffuka daban daban har 17 da ake tuhumarsa akai. Lauyoyinsa basu nemi beli ba.

A daren Alhamis aka kawo Guzman Amurka daga Mexico bayan da hukumomin kasar a wani matakin ba zata suka tusa keyarsa zuwa Amurka.

Guzman ya dauki fiyeda shekara yana adawa da shirin tusa keyarsa zuwa Amurka, bayan da tsere daga Fursina har sau biyu a kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG