Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nuna Majigin da Muryar Amurka Tayi Akan Rikicin Boko Haram


Kakakin rundunar sojojin Najeriya Birgedia Usman Sani Kukasheka
Kakakin rundunar sojojin Najeriya Birgedia Usman Sani Kukasheka

Majigin da Muryar Amurka ta shirya akan rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya wanda ya nuna illar da rikicin yayi, da aka fara nunawa a Abuja baban birnin taraiyar Nigeria, manyan mutane da suka hada da jami’an tsaron Najeriya sun halarci nuna majigin

Muryar Amurka ce ta shirya majigin akan tarzomar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya musamman a jihar Borno, jihar da ta kasance tamkar mahaifar Boko Haram.

Majigin ya nuna jajircewar ‘yan Najeriya musamman mutanen jihar Borno da wasu yankunan arewa maso gabas.

Majigin ya samu halartar kusoshin rundunonin sojin ruwa da na kasa da na sama. Akwai kuma manyan mutane daga ofishin mai baiwa shugaban kasar Najeriya shawara akan harkokin tsaro.

Kakakin hedkwatar sojojin Najeriya Birgediya Janar Usman Sani Kukasheka ya yaba da abun da Muryar Amurka tayi wajen gudanar da majigin. Yace kodayake Muryar Amurka na Amurka ne amma ta damu da abubuwan dake faruwa a Najeriya, musamman a arewa maso gabashin kasar. Injishi, majigin zai wayar da kawunan jama’a su san illar ta’addanci.

Aliyu Mustapha na Muryar Amurkan da yake Abuja domin majigin ya bayyana dalilan da suka sa aka gayyato kusoshin jami’an tsaro su ga majigin. Aliyu Mustapha ya ba da dalilai uku da suka sa aka gayyato jami’an tsaron. Yace na farko abokan aiki ne da gidan radiyon wajen fama da rikicin Boko Haram. Yace abu na biyu, kuma, duka sojojin suna da rawar da suke takawa ta fannin watsa labarai. Abu na uku shi ne su sojojin su san abun da su keyi da kuma kokarin da Muryar Amurka keyi domin taimakawa wajen ilmantar da duniya akan alamarin.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG