Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Canza Tunane da Dabi'a Ya Fara da Ni


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Yayinda shugaba Muhammad Buhari yake kaddamar da shirin "Change Begins with Me" a Abuja yau Alhamis takwas ga watan Satumba na shekarar 2016 yace sai mutum ya canza tunanensa da dabi'arsa za'a samu cigaba a kasa.

Shugaba Buhari yace daga kansa ne sauyin ko canijin ya fara wanda zai samar da cigaba a kasar ta Najeriya.

Muryar Amurka ta yiwa gwamnan jihar Bauchi tambaya akan yadda yake kallon kalamun shugaban kasa da shirin da ya kaddamar.

Barrister M. A. Abubakar gwamnan Bauchi yace a hakikanin gaskiya abu ne da yake da matukar mahimmanci saboda ita jam'iyyar APC tun lokacin da take yakin neman zabe abun da tayi ikirari a kai ke nan, wato ta kawo canji a kasar.

Yace a gaskiya canjin ba zai wakana ba sai duk ilahirin 'yan Najeriya sun canza tunanensu da halayensu da yadda yake ganin alamura. Sai hakan ya faru za'a cimma nasarar kawo canjin.

Kaddamar da shirin ya zo ne a daidai lokacin da ake korafe-korafen rashi da durkushewar tattalin arzikin kasa.

Muryar Amurka ta tambayi gwmnan jihar Imo Owelle Rochas Okorocha ko yana ganin canjin dabi'a zai yiwu a halin kunci da yunwa? Gwamnan yace maganar yunwa ba yau ta fara ba. Yace kamar gida ne da bashi da kwakwaran tushe. An dade ana lallabawa har aka kai yanzu. Yanzu abun da ya kamata a yi shi ne a sake gina gidan gaba daya. A sake sabuwar Najeriya, wato canji ke nan. Kodayake za'a samu wahala idan ana canji amma a yi domin a ji dadi nan gaba.

Shi kuwa shugaban hukumar wayar da kawunan al'umma na kasa Alhaji Garba Abari tsokaci yayi akan kaddamar da shirin. Yace babu wani fannin Najeriya da yau baya bukatar canji, canjin kuma wanda ba gwamnati kadai zata aiwatar dashi ba. 'Yan kasa da kansu zasu kawo canjin. Kowa ya binciki kansa. Idan ana batun cigaban kasa kowa ya tambayi kansa wane irin gudummawa zai bayar.

Madugun shirin canza dabi'a ministan watsa labarai Lai Muhammad yace shirin zai ilmantar da mutane akan mahimmancin kyautata dabi'u a duka yanayin rayuwa na kowane dan Najeriya.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG