Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Za Ta Binciki Wasu Gwamnonin Najeriya Bakwai


EFCC
EFCC

Wani babban aiki da shugaba Mohammadu Buhari zai tunkara bayan dawowarsa kan aiki, itace wata badakala da ta shafi wasu gwamnoni guda bakwai a Najeriya.

Shugaba Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin ci gaba da yakar cin hanci da rashawa da yayi katutu a kasar, wannan lamari dai zai zamanto wani babban abu da shugaban zai fara tunkara, wanda ya shafi gwamnoni bakwai kan wasu rarar kudi da aka dawo da su Najeriya, daga hukumar nan mai ba da basuka ta ‘kasa da ‘kasa, wato Paris Club.

Hukumar Paris Club ta mayarwa da Najeriya zunzurutun kudi har Naira Miliyan dubu 386, daga ciki ana zargin wadansu gwamnoni guda bakwai sunyi iya kansu da kudi har Naira Miliyan dubu 19. Kuma tuni hukumar EFCC ta ce ta gano Naira MIliyan 500 da suka shiga asusun wani gwamna wanda a halin yanzu ake ci gaba da gudanar da bincike.

Tun farko dai hukumar EFCC ta yi alkawarin bin kadun wannan badakalar da kuma tabbatar da ta yi cikakken bincike da rahoto ga gwamnati, domin a san irin matakan da za a dauka musamman a dai dai lokacin da ake kokarin cewar akwai wasu gwamnoni da suka saba alkawarin da aka yi da su da gwamnatin tarayya, dangane da kashe kudade na tallafi da aka baiwa jihohin, maimakon a biya ma’aikata albashi ko ‘yan fansho amma gwamnonin sun kashe kudaden ne wajen yin kwangila.

Mallam Garba Shehu, ya ce babu shakka wannan bayani yana dadin gaske ganin cewa hukumar EFCC tana gudanar da aikin ta, kuma shugaba Buhari ba zai ‘daga kafa ba gurin tabbatar da ganin an bi ‘ka’idoji na doka wajen ladabtar da duk mai hannu wannan badakala.

Domin karin bayani ga rahotan Umar Faruk Musa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG