Kafofin yada labaran kasar Senegal sun bada rahoton cewa shugaba Abdoulaye wade ya amince da shan kaye a zaben fidda gwani da aka gudanar jiya lahadi, kuma tuni har ya kira abokin takararsa domin taya shi murna.
Kwarya-kwaryar sakamakon zabe da kafofin yada labarai suke yadawa wanda ba hukumar zaben kasar ce ta bayar ba, ya nuna Mr. Sall yana da gagarumin rinjaye nesa ba kusa ba kan Mr. wade.
Za a dauki kwanaki kafin hukumar zabe ta sanar da cikakken sakamakon zaben. Tuni dai magoya bayan Mr. Sall suka cika titunan birnin Dakar suna murna.
Dubu dubatan ‘yan kasar ne suka kada kuri’unsu a zazzafar zaben fidda gwani tsakanin shugaban kasar dan shekaru 85 da haifuwa da tsohon Frayin minister, wadda galibin ‘yan hamayya suka bashi goyon baya.
Masu sa ido na kasa da kasa sunce galibi anyi zaben na jiya lahadi cikin tsanaki da lumana, koda shike ‘yan sanda sun harba borkonon tsohuwa a wata mazaba a Dakar babban birnin kasar, inda suka tarwatsa magoya bayan shugaba Wade jim kadan kamin ya iso domin kada kuri’arsa.
Tsarin Mulkin Senegal ya kayyade shugaba zaiyi mulki wa’adi biyu kacal,amma dagewar da Mr. wade yayin na neman wa’adi na uku ya janyo mummunar tarzoma cikin kasar.