ABUJA, NIGERIA - Uboh wanda ya ke sharhi kan mulkin shugaba Buhari na tsawon shekaru 8, ya ce da an bi shirye-shiryen da Najeriya ba ta bukatar cin dumbin bashi.
"Yanda fadar shugaban kasa ta ke aiki an kange shugaban daga abubuwa da dama, sau nawa na rubuta irin wadannan bayanai har ma da zantawa da mu ka yi da Muryar Amurka, amma 'yan hana ruwa gudu sun hana cimma gaci" Inji Uboh kan binciken da ya yi da ya kai ga gano harajin biliyoyin dala da ya dace wasu kamfanonin sadarwa da na fetur su zuba a aljihun gwamnati amma su ka ki yin hakan.
Uboh wanda kwamitocin kudi na Majalisar dokoki su sha gayyatar sa don bada bahasi, ya ce a hanyar kwarmato har garkame shi a ka yi a gidan yari na tsawon kwana 101 amma ya ce hakan bai karya ma sa guiwa ba.
Injiniya Magaji Muhammad Yaya da kan yi tafinta ga Uboh ya yi karin bayani, ya na mai cewa Najeriya na bukatar irin su Uboh don rufe kofofin zamba.
Idan za a iya tunawa, lokacin da gwamnatin Buhari ta kirkiro shirin kwarmato a wa'adin ta na farko, mutane da yawa sun sadaukar da kan su ga aikin amma bayanai na nuna yawanci sun kare ne tun su na kuka da hawaye har su ka zurawa sarautar Allah ido.
A lokacin mai taimakawa shugaba Buhari kan labaru Garba Shehu ya ce kusan dandalin tara bayanan kwarmato ba ya samun sakat.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya: