Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Me Ya Jawo Faduwar Farashin Mai a Kasuwar Duniya


Salihu Garba
Salihu Garba

Kafin watan Oktobar shekarar da ta gabata farashin mai a kasuwar duniya ya haura sama da dalar Amurka dari kowace ganga daya

Yau an wayi gari farashin ya fadi kasa fiye da abun da ake zato. Yanzu da kyar ganga daya ta kai dalar Amurka arba'in da bakwai.

A firar da nayi da Dr M.Kabiru Hassan na jami'ar Penn State ta jihar Pennsylvania nan Amurya ya lissafa wasu dalilai da suka sa farashin mai yayi tashin goron zabi da kuma dalilan da suka sa yanzu ya fadi.

Faduwar kasuwar hannun jarin kasashen Turai da Amurka a shekarun 2008 da 2009 ya sa gwamnatocinsu sun dauki wasu matakai domin farfado da tattalin arzikinsu. Misali, Amurka ta fito da wani shiri na baiwa bankuna da manyan kamfanoni, musamman kamfanonin dake kira motoci, lamunin miliyoyin dala bisa kan kudin ruwan da bai taka kara ya karya ba. Samun kusan kudin banza da bankuna suka dinga yi ya sa suka shiga harakar sayen mai firjanjan lamarin da ya sa kudin mai ya dinga tashi a kasuwar duniya. Kowane wata cikin shekaru biyun, wato 2008 da 2009, Amurka tana saka dala biliyan 85 cikin kasuwa. Na daya ke nan

Yadda tattalin arzikin kasar China ya habaka ya sa ta shiga sayan man fetur da yawa. Yawan man da take saya shi ma ya kara hawa-hawar farashin man. A daidai lokacin da China take wawurar mai a kasuwar duniya ita ma kasar Japan ba'a barta a baya ba.

Akwai dalilai kaman guda uku da suka jawo faduwar farashin man fetur. Cikin watan Oktoba din bara, wato 2014, shugabar babban bankin Amurka ta sanar cewa zata dakatar da saka dala biliyan 85 cikin kasuwa kamar yadda ta dauki shekaru biyu tana yi. Wannan sanarwar sai ta sa bankuna dake hada-hadar sayen mai a kasuwannin duniya suka yi taka tsantsan.

Dalili na biyu Amurka kanta ta soma anfani da wata sabuwar fasahar hako mai daga karkashin duwatsun kasa da na teku abun da ba'a iya yi ba da can. Wannan sabuwar fasahar ta sa Amurka na hako gangar mai miliyan tara kowace rana a jihohin North Dakota da Texas lamarin da ya sa ta daina sayen man Najeriya.

Dalili na uku, kasar Canada tana da mai wanda shi kasa yake jikawa. Hakarsa bashi da wuya. Kasar ake matsewa a fitar da man. Wannan ya sa shi man din yana da araha.

Wani sabon dalili kuma da ya fito yau shi ne furucin da mai baiwa gwamnatin Saudiya shawara akan albarkatun man fetur yayi. Yace kasar tana son farashin man fetur ya cigaba da faduwa daga nan har zuwa shekaru takwas. Ta riga ta adana dalar Amurka biliyan 800 domin kare rayuwar al'ummarta. Tana so farashe ya dinga faduwa har sai kasa kamar Amurka ta daina anfani da sabuwar fasahar nan ta hako mai daga karkashin duwatsu wadda tana da tsada. Ke nan idan kudin mai ya fadi Amurka ba zata ga anfanin sabuwar fasahar ba. Zata yi watsi da ita. Sai hakan ya faru Saudiya zata soma rage man da take hakowa domin farashin ya soma tashi.

A biyomu a shirinmu na Da Rashin Tayi domin cikakken bayani. Amma yanzu ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:09:50 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG