‘Yan Najeriya na kara nuna damuwa bisa rahotannin da ke fitowa daga arewa maso gabashin kasar na cewa mayakan Boko Haram sun kwace ikon garin Baga da ke jihar Borno.
Mutanen da ke fitowa daga garin na nuna cewa a halin yanzu mayakan na Boko Haram ne ke rike da garin, al'amarin da ke kara tayar da hankalin ‘yan Najeriya.
Mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, Shu'aibu Mungadi, ya ce akwai ban tsoro a ce yanzu Boko Haram sun fara korar sojoji suna kwace garuruwa irin su Baga.
A cewar masanin, "an yaudari Shugaba Muhammadu Buhari ko ‘yan Najeriya" musamman yadda a baya aka yi ta cewa an gama da ‘yan Boko Haram saura dan burbushinsu.
Sai dai rundunar sojin kasar ta Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa, mayakan na Boko Haram sun karbe ikon garin Baga.
“Wannan magana ba gaskiya ba ce, kamar yadda muka yi alkawari, za mu ci gaba da shaidawa jama’a abin da muke ciki,” in ji Kakakin sojin Najeriya Brigadier General Sani Usman Kukasheka, a wata hira da ya yi da wakilin Muryar Amurka, Haruda Dauda Biu a Maiduguri.
Ya kuma kara da cewa, “ya zuwa yanzu, sojojinmu suke gudanar da harkokinsu a wannan bangare, kuma za a ci gaba da ayyuka ba ma nan (Baga) ba, har zuwa wasu wuraren.”
Sai dai mai sharhi Mungadi, na tababar wannan ikrari na sojoji, yana mai cewa a baya har Shekau sun taba cewa sun kashe amma kuma batun ya zamanto ba haka ba ne.
Rahotannin farko da suka fito daga yankin na Baga, sun nuna cewa mayakan na Boko Haram sun karbe ikon garin Baga inda har aka bayyana cewa sun gudanar da sallar Asuba a cikinsa, bayan da suka far ma wani barikin soji a ranar Laraba.
Rundunar sojin kasar ta tabbatar da harin, amma ta bayyana cewa dakarun kasar sun fatattaki mayakan daga baya.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina da na Haruna Dauda Biu domin jin cikakken bayani: