WASHINGTON, DC —
Maimartaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Garbai El-Kanemi ya yabawa matasa masu farauto 'yan kungiyar Boko Haram a kokarinsu na kawo karshen ta'asar da kungiyar ke haddasawa.
Watanni biyu da suka wuce matasan Borno suka hada kansu suka shirya kana suka jaje wurin farauto 'ya'yan Boko Haram duk da cewa basa dauke da makamai kamar 'yan kungiyar. Jajewarsu ya sa jama'a na kiransu Fararen Hulan JTF wato suna gudanar da aikin tsaro da zakulo 'yan Boko Haram kamar jami'an tsaro na JTF.
Maimartaba Shehun Borno ya shaidawa Murya Amurka cewa matasan suna taimakawa kwarai wajan wanzar da zaman lafiya a Maiduguri da kewayenta. Ya ce akwai bukatar gwamnatocin karamar hukuma da na jiha da na tarayya su samarma matsan dake kuntunbala wajen farauto 'yan ta'ada aikin yi. Ya ce matasan kadan ne cikinsu ke da aikin yi. Yakamata a samar masu aikin yi kada daga baya a samu sabuwar matsala.
Daga bisani Shehun ya roki jama'a su yi hakuri su rungumi zaman lafiya. Ya yi fatan cewa wadanda suka bar garin ko jihar Allah zai dawo da su yayin da zaman lafiya ya dore.Basaraken ya ce akwai bukatar kara addu'a a duk fadin kasar domin samun zaman lafiya mai dorewa. Ya ce fiye da shekaru dubu da dari biyu ke nan da addinin Musulunci ya kafu a daular Borno. Sun tashi ne da Kur'ani da Musulunci. Babu wani abun da suka sa gabansu. Sabili da haka ya roki gwamnatin tarayya ta taimakawa mutanen Borno domin wahala da suka sha sanadiyar tashin tashina da ya kwashe fiye da shekaru uku ana yi.
Haruna Dauda Biyu nada karin bayani.