Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shawo Kan Cin Hanci Da Rashawa A Najeriya


Nigeria Anniverasry
Nigeria Anniverasry

Zauran matasa wakilinmu Murtala Faruk, yajiyo ra’ayoyin wasu matasa a sokoto domin jin yadda gwamnati mai zuwa zata sauke nauyin akawarurrukan data ‘dauka lokacin yakin neman zabe.

Ganin cewa sai da kudi mai yawa gwamnati zata iya sauke nauyin dake kanta koyaya za’ayi a samar da kudaden ganin cewa Najeriya bata da kudi, ga tulin bashi, ga karyewar darajar man fetur yanzu a duniya.

Murtala yaji ta bakin Alhaji Murtala ‘Dan Baba da sauran wasu matasa, wadanda suke ganin indai aka kashe matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya, to tabbas za’a shawo kan duk wata matsala da kasar ke fuskanta cikin sauki, a ganinsu cin hanci shine makasudin bashin da ake bin kasar Najeriya, idan aka duba irin albarkatun da kasar ke dasu.

‘Daya daga cikin matasan ya nuna yadda yake tausayawa shugaba mai jiran gado Mohammadu Buhari, kasancewar akwai matsaloli da dama da kasar ke fuskanta a halin yanzu, ya zama dole sai shi shugaban mai jiran gado yayi taka tsantsan wajen gudanar da ayyukansa domin yanzu ba lokacin mulkin soja bane lokaci ne na siyasa.

A ra’ayin shikuma wani matashi na ganin cewa hana cin hanci da rashawa, da samar da wutar lantarki sune abu na farko da gwamnati zata fara aiki akai, bayan haka kuma duk sauran matsalolin kasar za’a iya shawosu cikin sauki da kwanciyar hankali.

XS
SM
MD
LG