Addinin musulunci ya shawarci da ‘karfafa gwiwar namiji da zai iya yin auren mace fiye da guda ‘daya, amma sai aka ja kunnen namiji cewar in yaga bazai iya ba to ya hakura da guda ‘daya, in kuma bazai iya guda ‘dayar ba to ya sami baiwa ya saka ta a daki, domin nauyin dake kan baiwa bai kai nauyin matar da aka ‘daura masa aure ba.
Sharudan aure ya kasu kashi kashi akwai sharudin daya shafi wadata, mutum yana da wadatar da zai iya yi missali sukunin muhalli, ciyarwa, sitira, ‘daukan nauyin kula da lafiya.
Sharadi na biyu karfin zuciyar yin shari’a a tsakaninsu, tsayar da hukunci, da tabbatar da adalci. Kasancewar ba kowane keda zuciya mai ‘karfi da zai iya yin shari’a ba.
Sharadi na uku mutum ya tabbatar zai iya raba wa matansa lokaci, tare da adalci, yana kuma da dama da lokacin da zai iya kasancewa da kowacce matarsa ya kuma basu irin soyayyar da suke bukata.
Karfin sha’awa ta saduwar aure da zai iya zagaye duk matansa a cikin wani lokaci yana rayuwar aure da su, kasancewar kowanne namiji yasan iyaka gejin sa, yasan iyakar abinda zai iya yi yasan iya abinda bazai iya ba, to idan mutum yasan bazai iya ba to bashi da amfani yaje ya karo aure, ya ‘daurawa kansa karin nauyi.
Daga karshe sai mutum ya san ilimin aure, kan yadda zai iya gudanar da gidan sa da matansa kafin ma ya fara tunanin ka auren mace fiye da ‘daya.