Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sha'awar Aikin Jarida Yasa Nayi Karatu Mai Zurfi


Baraka Salisu
Baraka Salisu

A kowanne irin abu da dan adam yake a rayuwa yana tattare da nashi irin kalu balen, a lokacin da nake jami'a kalubale da na fuskanta shine, na wasu malamai kan sanya darasi wanda baya cikin tsari manhaja da aka fitar dashi tun daga farko, inda a mafi yawan lokuta hakan kan shiga hakkin dalibai, a ta baki wata matashiya malama Baraka Salisu.

Kamar sauran matasa Baraka, bata fuskanci matsala ba a fanni neman gurbi na karatu, domin kuwa abinda take nema shi ta samu a jami'a, kuma ta kammala karatunta ne ba tare da ta samu wata matsala ba a fannin karatu ko daga wajen malamai.

Ta ce babba abin sha’awa shine yadda mata suka maida hankali a harkar neman ilimi, duba da yadda a da ba’a damu da neman ilimi ba, a yanzu abin ya sauya mata na kokarin kawo cigaba a alummarsu ta hanyar jajircewa, da marawa 'yaya da iyaye ke yi wajen neman ilimi.

Baraka ta ce daga cikin abubuwan da suka ja hankalinta har ta karanci aikin jarida, shine yadda take ganin aikin na sauya alkibilar alumma tare da kawo canji. Tana fatar a gaba ta bada nata irin gudunmawar wajen ganin ta kawo cigaba ga al'ummar ta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00
  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG