Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NDLEA Ta Kama Wata Mata Da Ake Zargi Da Yunkurin Safarar Hodar Iblis Zuwa Pakistan


Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa.
Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar dauke da sa hannun Daraktan yada labarai, Femi Babafemi, ta ce an kama Chisom da hodar iblis da nauyinta ya kai kilo 8.

Hukumar NDLEA da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi Najriya, ta ce ta cafke wata mata ‘yar kasuwa da ake zargi da hada kai da wasu ‘yan kasar Pakistan wajen safarar hodar iblis zuwa Lahore, babban birnin Pakistan.

Matar mai suna Okefon Darling Chisom, ta shiga hannun jami’an na NDLEA ne a filin tashi da saukar jirage na Legas da ke kudancin Najeriya.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar dauke da sa hannun Daraktan yada labarai, Femi Babafemi, ta ce an kama Chisom da hodar iblis da nauyinta ya kai kilo 8.

NDLEA ta ce Chisom ta boye hodar iblis din ce a cikin na’urar amsa kuwwa, yayin da take kokarin hawa jirgin kamfanin Qatar Airways zuwa Lahore inda za ta ratsa ta Doha a ranar Asabar 5 ga watan Nuwamba.

Bincike ya nuna cewa matar ta na da alaka da wasu ‘yan Pakistan biyu da suka hada da Asif Muhammad mai shekaru 45 da Hussain Naveed mai shekaru 57

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG