Na fara sana’ar hannu ne sakamakon ganin wata ‘yar uwa ta mace da na ga ta jajirce tana yi kuma sana’ar ta rufa mata asiri hakan ne ya sa na dukufa domin yin tawa sana’ar ta haja wato sayar da atamfofi, mayafai da kayan shafe-shafe na mata kuma na tabbatar da ana samun riba mai yawa inji malama Murja Illiyasu Ba’awa.
Malama Murja ta kara da cewar sana’ar hannu ta sa ta tsaya a kan kafafunta ba tare da ta nema a wajen wani ba ta hanyar yar murya ko roko, sannan tana samun kasuwarta ne ta hanyar makwabta, ta haka ne aka santa da kuma sana’ar da take yi.
Matashiyar ta ce baya ga haka tana hadawa jama’a lefe da zarar bukatar hakan ta taso, sa’annan tana sayar da dukkanin kayayyakin da ake hada lefe da su
Har ila yau tana taimakawa al’ummarta daga cikin ribar da take samu da zarar ta sayar da kayanta a matsayin sadaka, ta taimakawa masu kananan sana’oi ko mara karfi domin su farfado su zamo masu dogaro da kai.
Daga karshe Murja, ta ce babban burinta kamar mai gidanta ta gina wasu mata domin su ma su zamo masu dogaro da kansu suma su tsaya a kan kafafunsu, sannan ta ce ita bata bin doguwar ribar da zarar zata samu ko kadan ce ta isheta.
Facebook Forum