Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanatocin Amurka Biyu Sun Kara Akan Wadanda Trump Yake Son Ya Nada


Sanata Lindsey Graham,dan Republican daga jihar Carolina ta Arewa wanda ya kara da Sanata Ryan Paul shi ma dan Republican daga jihar Kentukey
Sanata Lindsey Graham,dan Republican daga jihar Carolina ta Arewa wanda ya kara da Sanata Ryan Paul shi ma dan Republican daga jihar Kentukey

Senatocin Amurka biyu, sun-kara jiya Lahadi, gameda mutanen biyu da shugaba Donald Trump ya zaba, watau Mike Pompeo, darektan hukumar leken asiri na Amurka watau CIA , ya zama sabon sakataren harkokin wajen Amurka, yayinda Gina Haspel, zata karbi ragamar iko, a hukumar ta CIA.

Idan har majalisa ta amince da nadinta, Haspel zata zama mace ta farko da zata jagoranci hukumar CIA a tarihin hukumar na tsawon shekaru 70.

Senata Lindsey Graham, mai wakiltar jahar Carolina ta Arewa, yayi hasashen duka mutanen biyu zasu sami amincewar majalisar dattijai. Yayi watsi da takwaran aikinsa Senata Rand Paul daga jahar Kentucky, a "zaman "saniyar -ware" tsakanin sauran senatoci 'yan Republican.

Shi ma Senata Paul a cikin shirin na CNN, ya bayyana adawarsa da nadin Pompeo, saboda yana goyon bayan Amurka ta jagoranci juyin mulki a wasu kasashe. Yayinda Gina Haspel kuma, ana alakanta ta da cin zarafin mutane da ake tsare da su kan zargin ta'addanci a wasu wurare kebabbu a kasashen waje.

Senata Paul yace zai yi iya kokarinsa na ganin basu kai labari ba a majalisar dattijan, inda senatoci 'yan Republican suke da 'yar karamar rinjaye; senatoci 51-yayinda Democrat suke da wakilai 49.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG