Shugaban Kungiyar malaman Jami’ar Dr Ibrahim Magaji Barde yace akwai bukatar ‘yan Najeriya su taimakawa ‘yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita a arewa maso gabashin kasar.
Dr Barde ya yi wannan kiran ne lokacin da yake mika agajin kayan abinci ga wadansu ‘yan gudun hijira da rikicin Boko Haram din ya daidaita a garin Maiduguri. Ya bayyana tausayawa ‘yan gudun hijiran da ya gani a sansanoni dabam dabam a garin Maiduguri, ganin irin halin da ya samesu ciki, musamman ma rashin makwanci mai kyau, da ruwan sha, da ababan more rayuwa irin na yau da kullum.
Shugaban kungiyar malaman jami’an yace halin da ‘yan gudun hijiran ke ciki bai fi karfin ‘yan Najeriya ba idan zasu bada tallafi ko da kadan- kadan ne, zai taimakawa ‘yan gudun hijiran wajen gudanar da rayuwarsu kamar sauran al’umma.
A cikin hirarsu da Sashen Hausa, Dr Barde ya bayyana cewa, sun kai tallafin kunshin kayayyaki dubu uku da dari biyar da za a rarrabawa ‘yan gudun hijiran, da kiyasin kudin ya kai miliyan biyar. Ya bayyana cewa, malaman jami’ar sun rika bada gummuwar naira dubu daya kowannensu na tsawon watanni uku, suka hada kudin suka sayi kayayyakin tallafin, ya kuma yi kira ga sauran jami’oin da makarantun kimiyya da fasaha suma subi sawu.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu Haruna Dauda Bi’u ya aiko mana.
Facebook Forum