A cikin shirin mu na wannan makon, mun tattauna da wasu matasa maza da mata, kuma sun bayyana mana ra’ayoyin su akan wata sabuwar dabi’ar da ake kira (Wankan Yamma) da kuma Wankan Karas!
Wankan yamma kamar yadda matasan suka bayyana, samari da ‘yan mata kan yi wanka da yamma ne kuma su sa kaya masu kyau sa’annan su fita yawo cikin unguwa da tunanin haduwa da sababbin masoya.
Shi kuma wankan Karas samari maza ne kadai ke yi, dalili kuwa shine irin kayan da samarin ke sawa ne yasa ake kiran sa wankan karas, wato wando mai kama da karas, sama da fadi kasa tsududu.
A cikin samarin da muka zanta da su, sun bayyana mana cewar yawanci sukan sami ‘yan matan ne a yayin da suke zaune zaune a majalisa ko kofar gidajen su, kuma sukan nemi yin abuta da su musamman ma idan budurwar ta iya kwalliya. Wasu samarin sun bayyana cewa suna da ‘yan mata fiye da goma da suke haduwa da yamma kuma ko wacce da lokacin da ake ganinta.
Da muka koma bangaren ‘yan matan, suma sun nuna cewar hakan take, wato sukan yi wannan kwalliya ne domin fita cikin unguwa da tunanin ko za su dace su hadu da samarin kwarai, zamani ina zaka kaimu!
Abin tambaya a nan shine; a ina wannan sabuwar dabi’ar ta samo asali?
Saurari cikakkiyar hirar. dandalinvoa.com