Haka kuma ana ra san karin wasu mutane miliyan biyu zasu rasa aikinsu a karshen wannnan shekarar. Wannan mummunan labari na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ta wuce kasar Indiya inda ta zamanto kasar ta fi yawan mutanen dake fama da talauci a duniya, gabannin zaben shugaban kasar da ke tafe a watan Fabarairu.
A watan Satumbar shekarar da ta gabata Najeriya ta fita daga cikin matsalar tattalin arziki mafi muni da ta taba fuskanta cikin shekaru talatin, inda yanzu ake fatan ta samu farfadowa.
Amma rashin aikin yi da talauci na ci gaba da samun gindin zama a kasar da kashi arba'in cikin dari na al'ummar kasar miliyan dari biyu ke fama da rashin aiki kwata-kwata.
Najeriya na bukatar ta kirkiro ayyukan yi Miliyan hudu a duk shekara, idan har ana son fita daga cikin wannan kangi, wanda ke zama babban kalubale ga duk wanda ya sami nasarar lashe zaben na watan Fabarairu.
Facebook Forum