Yayin wani jawabi da ya yiwa manema labarai a hedkwatar NATO da ke Belgium, Mattis ya ce, yunkurin dawo da Rasha kan layi bisa wannan yarjejeniya da ta sa hannu, na da muhimmanci.
Ita dai Amurka ta dage cewa Rasha na fitar da makamai masu linzami wanda hakan ya sabawa yarjejeniyar, wacce ake wa lakabi da INF a takaiace.
Wannan yarjejeniya dai ta haramta fitar da makaman nukiliya masu linzami, wadanda ke tafiyar matsakaicin zango akan doron kasa.
Rasha a nata bangaren, ta sha musanta wannan zargi da ake cewa ya sabawa yarjejeniyar ta INF, sannan ita ma ta zargi Amurka da sabawa wannan shiri.
Hukumomin Moscow sun yi zargin cewa za a iya kai musu hari da makamai masu linzamin da Amurka ta girke a Poland da Romania idan aka inganta musu fasali.
Facebook Forum