Wani binciken cibiyoyi masu zaman kansu da aka gudanar a kan tarzomar da ta barke cikin watan Yulin da ya gabata a Sudan ta Kudu ya gano cewar rundunar kwantar da tarzoma ta Majalisar Dinkin Duniya ko MDD da sojojin kiyaye sulhu sun gaza wurin kare fararen hula da ma’aikatan agaji.
Wani kakakin MDD yace babban Sakataren MDD Ban Ki-moon ya bukaci a canza komandan sojojin zaman lafiyar na MDD dake aiki a Sudan ta Kudu.
Wannan fada tsakanin sojojin gwamnatin shugaba Salva Kiir da rundunar masu biyayya ga madugun yan adawa Riek Machar ya barke ne a ranar takwas ga watan Yuli kusa da fadar shugaban kasar. Wasu rahotanni sun ce mutanen da aka kashe a rikicin sun kai 300.
MDD dai tana da sojoji sun kai 14,000 dake Sudan ta Kudu. A birnin Juba, akwai sojojin kasashen China da Ethiopia da Nepal da kuma Indiya dake aiki a wurin a lokacin tarzomar.