Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kasashen Majlisar Dinkin Duniya Sun Jefa Kuri'ar Haramta Makaman Nukiliya


Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon

Wakilan Kasashe a Majalisar Dinkin Duniya ko MDD sun kada kuri’un haramta makaman nukiliya.

A ranar Alhamis ne kwamitin karbe makamai da kuma tsare tsare na kasa da kasa a Majalisar Dinkin Duniya sukayi zabe kan tabbatar da hanyar da za’a tattauna akan dokar da zata haramta makaman Nukiliya , duk da rashin goyon bayan kasashe da ke da karfin Nukiliya din.

“Beatriz Fihn, babban Daraktan Kemfen na kasa da kasa kan Watsar da Makamin Nukiliya yace “Wannan Alkawari ba zai kawar da Makaman Nukiliya dare daya ba . Amma zai kafa hanya mai karfi da zata haifar da tsayayyar doka ta kasa da kasa da Tsangwamar Makamin Nukiliya da zata sa kasashen da suke da Makaman su yi watsar da su.

Fihn ya kara da cewa wannan zabe ya kafa tarihi duk da dai zai yi wahala kasashen su daina amfani da makamashinsu na Nukiliya.

Kasashen da suka gabatar da Makalar da ba’a kare taba sun hada da Austria, Brazil, Ireland, Nigeria, Mexico, da Afirka Ta Kudu. Kasashe 123 ne suka saka mata hannu yayin da 38 suka ki, sai kuma 16 da basu da matsaya. Daukacin kasashen da suke da karfin makamin Nukiya sun hau kujerar naki.

XS
SM
MD
LG