Sakataren Tsaron Amurka Chuck Hagel ya ce barazanar da masu tsattsauran ra'ayi na Daular Islama ke wa tsaron duniya baki daya, ya wuce duk wani abin da aka taba gani.
Da ya ke jawabi a jiya Alhamis a birnin Washington, Hagel ya bayyana 'yan bindigar da cewa kungiya ce da ta zarce ta 'yan ta'adda na yau da kullum. Ya ce kungiyar ta fi duk wata kungiyar ta'addanci da aka taba yi makamai da dabarun yaki da kuma kudi.
"Su na matukar barazana ga duk wani muradinmu, walau a Iraki ko ma a duk wani wuri." inji shi.
Hagel na jawabin ne ganga da Hafsan Hafsoshin Amurka, Janar Martin Dempsey, wanda ya bayyana kungiyar ta Daular Islama da cewa "su na da hankoro salon na karshen duniya."
Janar din ya ce za a iya cin kungiyar da yaki, to amma sai idan an far ma ta a Syria da Iraki. Ya yi hasashen cewa za a iya kawar da al'adar gwagwarmaya da makami ce kawai idan mutanen yankin masu yawan miliyan 20 da ke takure a wannan babban yankin, tun daga birnin Damascus zuwa birnin Bagadaza.