Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran za ta Yarda a Saka Ido Akan Shirin ta na Nukiliya


Shugaban Iran Hassan Rouhani (File Photo)
Shugaban Iran Hassan Rouhani (File Photo)

Iran ta ce za ta yarda a saka ido kan shirin ta na nukiliya kamar yadda yake a cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya a duniya.

Iran ta ce za ta yarda a saka ido kan shirin ta na nukiliya kamar yadda yake a cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya a duniya, amma ba za ta lamunta da wani binciken da ya zarce wannan ba.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ce duk wani binciken da ya ketara iyakacin abun da doka ta kayyade a cikin yarjejeniyar, zai zama wani sabon abu na cin mutuncin muradun duka kasashe masu tazowa.

Mr. Rouhani ya fadi hakan ne a birnin Tehran lokacin da yake ganawa da Yukiya Amano shugaban hukumar kula da makaman nukiliya ta Majalisar dinkin duniya.

Amano ya ce tattaunawar ta yi amfani kuma ya ce ya ji dadi da Iran ta yi alkawarin bada hadin kai wajen warware batutuwa game da shirin ta na nukiliya.

Amuurka da kawayen ta na yammacin duniya sun dade su na zargin Iran da neman mallakar makamin nukiliya, amma Iran ta ce shirin ta na nukiliya ba na yaki ba ne. Iran na neman a dage ma ta takunkumin karya tattalin arzikin da kasashen yammacin duniya suka kwakuba ma ta da nufin tilasta ma ta, ta yi watsi da duk wani kokarin neman kera makamin nukiliya.

XS
SM
MD
LG