An fara kiyaye wannan ranar ne a 1868, shekaru uku bayan ƙarshen Yaƙin basasar Amurka. Ranar Tunawa da mazan jiya da ada, ake kira ranar lika lambar yabo,ba ana nufin tunawa da ranar wani takamaiman yaƙi na musamman ba , amma a maimakon haka yana nufin ƙarfafa 'yan ƙasa su tuna da sadaukarwar waɗanda suka mutu waɗanda aka binne a garinsu, kuma don girmama waɗannan matattu da suka mutu sanadiyar yaki ta hanyar yin kawata kaburburansu da furanni.
A ranar wannan bikin na farko, wasu mutane 5,000 sun kawata kaburburan sojojin da su ka yi yakin basasa 20,000 da aka binne a makabartar Arlington ta kasa da ke Washington DC, ba tare da la’akari da bangaren dasuka yi yakin ba. Taron ya zama al'ada wanda ya bazu ko'ina cikin ƙasar.
A yau, birane da garuruwa a duk faɗin ƙasar suna bikin Ranar Tunawa da yin fareti waɗanda suka haɗa da ma’aikatan soja da mambobin kungiyoyin tsofin sojoji. Mutane suna zuwa makabarta da wuraren tunawa da mazan jiya. Yayinda wasu suke sanya ƙananan furanni don tunawa da yaƙin.
Wannan al'adar ta fara ne a lokacin Yaƙin Duniya da wata waƙa da wani soja ya rubuta don tunawa da wani abokinsa da ya mutu a Ypres, da ke Faransa a farkon Mayu 1915, kamar dai yadda fararen furanni masu launin ja suka fara bullowa a cikin filaye, kuma a kan kaburburan wadanda suka mutu.
Don haka, a kowacce ranar Tunawa da Mutuwar,ana jera kananan tutoci da furannin masu launuka iri-iri kan manyan duwatsu da alamomin tunawa a makabarta a duk fadin kasar, domin kawata kaburburan jaruman sojoji. Kuma suna saka ƙananan jan furani da ake sawa don tunawa da sojojin da suka mutu wajen kare ƙasarsu da manufofinta. Sun mutu ne suna kare hanyar rayuwa, da abinda suka yi imani da shi, kuma girmamawar da suka samu ta sadaukarwar su tana tare da su har abada.