Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karramawar Ban Girma Ga Matasan Mawakan Kasar Hausa


A makon da ya gabata ne kamfanin Two Slaves Records suka bada lambar girmamawa ga wasu mawaka guda biyu, wato Bello Ibrahim wanda aka fi sani da Billy O da Dabo the prof inda suka basu girmamawa na Best Hausa hip hop icon.

Wannan award din dai tarin matasa mawaka ne suka shirya shi domin nuna godiyarsu da yabawarsu ga wadannan gwarazayen na wakokin hip-hop dangane da yadda suke mara musu baya.

Billy O ya ce ya ji dadin karramawar a cewarsa hakan na nuni da cewar an yaba da ayyukansu, da kuma irin gudumuwar da suke baiwa waka ta hip hop, shi kuwa Dabo the prof cewar yayi idan mutun yayi hakuri a rayuwa zai ci ribar abinda yake yi.

Umar Ayuba Isah wanda aka fi sani da Dabo the prof ya kara da cewa abin alfahari ne a matsayin shi na mawaki ya ga cewar yana taba rayuwar wasu matasa, tare da cewa wannan irinsa shine na farko da matasan mawaka suka yi masa.

Jagoran bada lambar girmamawan Suleman Aliyu yace mawakan guda biyu suna yawan bibiyar ayyukansu, tare da basu himma da karfin gwiwa wajen cimma muradansu hakan ne ma ya sa suka shirya wannan shirin na girmama mawaka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:15 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG