Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Kwamitin Binciken Rigimar Makiyaya Da Manoma A Jihar Adamawa


An kafa wani sabon kwamiti da zai binciki rikece rikicen da aka samu tsakanin Fulani Makiyya da Manoma a wasu yankunan jihar Adamawa, lamarin da ya jawo asarar rayuka da yawa har ma da raba wasu daga gidajensu.

Kwamishinan yada labaran jihar Ahmed Sajo, yace an kafa kwamitin ne don bincikar al’amarin, kuma duk rahotan da kwamitin binciken fitar tabbas za a yi amfani da shi wajen kawo karshen rigimar, da kuma kare faruwar makancin wannan tashin hankali da ka iya bullowa nan gaba.

A makon jiya ma an samu wani tashin hankali a yankin Kidimu dake karamar hukumar Demsa, inda rayuka fiye da goma suka salwanta bayan da wanda ya faru a karamar hukumar Girei duk dai a jihar Adamawa.

Kawo yanzu dai masana na ganin dole ne sai gwamnatoci a Najeriya sun tashi tsaye wajen magance wannan matsala da ake samu tsakanin Fulani Makiyaya da kuma Manoma, wadanda ke zama tamkar ‘dan Juma ne da ‘dan Jummai.

Saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz daga Yola.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG