Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Direbobi Sun Katse Hanyar Abuja Zuwa Kaduna


Direban da 'yansanda suka cire wa hakori saboda ya ki ya basu nera dari biyu akan hanyar Abuja zuwa Kaduna
Direban da 'yansanda suka cire wa hakori saboda ya ki ya basu nera dari biyu akan hanyar Abuja zuwa Kaduna

Direbobin motocin haya sun katsehanyar Abuja zuwa Kaduna biyo bayan dan karen dukan da dayansu ya sha a hannun 'yansanda saboda ya ki ya bada cin hancin nera dari biyu

Hayaniya ta biyo bayan direbobi sun dakatar da zirga zirgar motoci akan hanyar Abuja zuwa Kaduna daidai Zuba sanadiya dukan da 'yansanda suka yiwa wasu direbobi.

A wurin binciken ababen hawa ne a Zuba lamarin ya faru yayinda 'yansandan suka bukaci wani direba ya basu cin hancin nera dari biyu da shi kuma ya ki ya bayar. Kin basu ya kaiga dukansa har suka cire masa hakori.

Wakilin Muryar Amurka ya iske direban cikin jini tare da karamin wando. Wani direban ma yace an kusa karya masa kafa. Masifa ta yi yawa, inji shi.

Jerin gwanon motoci
Jerin gwanon motoci

Direbobin sun bukaci a cire masu 'yansanda saboda azabar da suke sha a hannunsu.

'Yansanda sun ki su ce komi domin wai ta lafiyar direban suke yi, wato direban da suka lakadawa dan karen kashi.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG