Bayan an kafa kwamitocin karbar mulki a ranar 29 ga watan gobe na mayu a matakai daban-daban, yanzu hankali wasu ‘yan najeriya ya fara karkata kan hasashen yadda alaka zata kasance tsakanin ‘yan majalisar dokoki da gwamnonin jihohi, musamman a jihohin Kano da Sokoto, inda Jam’iyyar APC ta lashe dukkanin kujerun majalisun dokokin.
Wakilinmu na shiyyar Kano, Mahmud Ibrahim Kwari ya lura cewa tun bayan dawowar mulkin dimokaradiyya aka shiga zargin ‘yan Majalisun Dookin jihohi da zama ‘yan anshin shatan gwamnonin jihohi, al’amarin da su kuma gwamnonin ke daukawa a matsayin kyakyawar fahimta tsakanin bangarorin gwamnati.
To saidai gwamnan Kano mai jiran gado Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya ce muddun ‘yan Majalisar Dokoki sun fahimci alkiblar da ake fuskanta da kuma inda aka dosa to ba su cikakken iko ba abu ne mai wuya ko ba. Ya ce da muhimmanci a ba kowane bangare damar yin aikinsa. Umar Haruna Doguwa, Shugaban APC na jihar Kano ya ce wannan karon fa za a ga banbanci dangane da barin kowa ya yi aikinsa. Shi ma Honorabul Abba Ibrahim Garko ya ce fitowa daga jam’iyyar guda ba za ta sa Majalisa ta goyi bayan bangaren zartaswa a maimakon kare muradun jama’a ba.