Rundunar tace tayi anfani da wasu bayanan siri wajen cetosu. Rundunar ta kuma kama wasu da ake zarginsu da sato yaran.Kwamishanan 'yansandan Abia Adamu Ibrahim Kanoma ya tabbatar da aukuwar lamarin. Yace idan sun sato yaran wasu 'yansanda sukan tsaya a matsayin masu son su sayi yaran ta hakan sai a kamasu. Ta haka suka kama wadanda suka sato yaran daga Delta.Sun kama wadanda suka sato yaran da wadanda suka sayarwa duk suna hannun 'yansanda.
Kwamishanan yace ya zagaya al'ummomin jihar domin neman hadin kansu dangane da sace mutane da kuma nuna bata gari dake fakewa cikinsu suna aikata miyagun laifuka. Sun ba alummomin lambobin 'yansanda da zasu iya kira su basu labari cikin siri ba tare da bayyana kansu ba da zai taimaka wurin gano bata gari kafin su aikata barna. Yace harkar tsaro yanzu harka ce da ta shafi kowa da kowa.
Al'ummomin jihar ta Abia sun yi na'am da kiran kwamishanan kuma sun ce a shirye suke su bada hadin kai. Zasu bada duk wani labari da zai taimaka musamman ganin yadda kasar take.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.