Su dai masu zanga zangar lumana din suna yi ne domin matsawa gwamnatin kasar ta kara karfi da karfe ta ceto 'yan matan da aka sace. Yayin da yake jawabi Christopher Smith yace ya zo ne domin ya tattara bayyanai da suka shafi fataucin mata a Najeriya da kuma taimako da yakamata a ba kasar wajen ceto 'yan matan Chibok.
Christopher Smith yace ya gana da 'yan majalisun Najeriya da shugabannin kwamitoci da wasu shugabannin addinai yace kuma ya samu bayyanai sosai. Yace to saidai sun lura cewa ta'adanci na karuwa a duk fadin duniya maimakon ragewa duk da kokarin da a keyi a wurin maganceshi.
Christopher yace zai koma Amurka su sake zama a kwamiti su gabatar da rahoto akan ziyararsa. Yace amma fa a tuna alhakin ceto 'yan matan ya rataya ne akan mahukuntan Najeriya.
Nasiru Gambo daya daga cikin masu zanga-zangar a ceto 'yan matan Chibok yace sai fa an canza salo. Yace wannan lamarin zai cigaba da faruwa har sai gwamnati ta daina dora laifi akan wasu ko wani abu an fuskanci anihin ita matsalar da gasken gaske. Shugabannin yanki da na kasa yakamata su ajiye addini da siyasa da kabilanci gefe daya su yadda da matsalar. Matuka ba'a yi haka ba, ba za'a cigaba ba.
Ga rahoton Medina Dauda.