Hukumomi a Najeriya sun dauki sababbin matakan tsaro a Abuja babban birnin kasar bayan kazamin harin bom da aka kai a shelkwatar ‘yansandan kasar. Jami’an gwamanati a babban birnin kasar sun bayyana matakan tsaron da za a dauka a wuraren da jama’a da dama ke taruwa, a wata sanarwa da suka bayar yau Laraba. Yanzu an bukaci gidajen barasa da gidajen silma dake birnin tarayya Abuja su rufe da karfe goma na dare. Yayinda za a rufe wuraren da kananan yara ke taruwa da suka hada da wuraren wasan yara da filayen shakatawa su rufe da karfe shida na yamma. Hukumomi sun kuma hana ajiye motoci a kan wadansu manyan hanyoyi biyu inda ofisoshin gwamnati suke. Jami’ai a birnin tarayya Abuja sun ce daukar wadannan matakan ya zama tilas domin tabbatar da kare kaddarorin gwamnati.
Hukumomi a Najeriya sun dauki sababbin matakan tsaro a Abuja babban birnin kasar bayan kazamin harin bom da aka kai a shelkwatar ‘yansandan kasar.