Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya Ta Karyata Rahotan Amnesty International


Wasu mutane da sojoji ke tsare da su a Barikin Giwa.
Wasu mutane da sojoji ke tsare da su a Barikin Giwa.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta fitar da rahotan dake cewa, a kalla mutane 149 ne da suka hada da mata da kananan yara suka mutu a Barikin Giwa dake garin Maiduguri a jihar Borno. Sakamakon azabtarwa da yunwa da rundunar sojan ke barinsu da shi.

Kungiyar dai tace ta sami wannan kididdiga ne tun daga watan Janairu zuwa watan Afrilun wannan shekara, duk da yake kungiyar ta bayyana cikin shafinta na yanar gizo cewa basu da sahihin tabbaci game da wannan bayanai da suka wallafa. Tace andai jibge gawarwakin mutanen ne a dakunan ajiye gawarwaki dake cikin asibitoci a garin Maiduguri.

Daga bisani aka binne su a wasu makabarta, wanda kuma tace akwai bukatar daukar matakan gaggawa. Haka kuma kungiyar tayi zargin cewa akwai kananan yara 12 wanda suka hada da mata da jarirai 4 da basu kai shekara guda ba.

Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda, ya tuntubi Birgediya janal Rabe Abubakar, mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, inda yace, “Gaskiya lamari abin ya bamu juyayi, saboda bayan wadannan mutane sun fito da nasu rahoto kwanakin baya, muka gayyacesu domin su ga inda muke ajiye mutanen, har suka bamu shawarwari masu kyau har muka dauka muka kuma gabatar da duk abinda suka shawarcemu.” Ya ci gaba da cewa sai gashi daga baya sun fitar da wannan rahoto.

Daga karshe Birgediya Rabe, yace wannan makirci ne irin nasu kuma ba mamaki wani buri suke son su cimma, amma su a masayinsu na jami’an tsaro da sojojo suna nan suna kokarin tabbatar da cewa yadda sukayi kokarin shiga Dajin Sambisa, to suna son kawo karshen wannan yaki da nasara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:43 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG