Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Civil Defense Ta Lashi Takobin Hukunta Jami’inta Da Ake Tuhuma da Safarar Alburusai


Civil Defense Zamfara
Civil Defense Zamfara

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara, ta bayyana kaduwar ta dangane da kama daya daga cikin jami’an ta, ASCII Maikano Sarkin-Tasha, wanda rundunar ‘yan sandan jihar ta tuhume shi da laifin safarar alburusai da kwayoyi zuwa ga ‘yan bindiga.

A wata zantawa da manema labarai, kwamandan Civil Defense na jihar Zamfara, Sani Mustapha, ya tabbatar da kama Jami'in tare da jaddada cewa rundunar na da kima da martabar da ba zata bari bara-gurbi su lalata ba, tare da bada tabbatacin cewa hukumar zata ci gaba da tabbatar da gaskiya a aiyukan ta, tare da kiyaye ka’idojin aiki.

Kwamandan, Sani Mustapha ya kara da cewa, a baya an kai karar Sarkin-Tasha da cewa ba ya zuwa Wurin aiki na tsawon lokaci kafin ‘yan sandan su tsare shi.

A cewar shi, binciken farko da suka yi ya nuna cewa an kama Sarkin-Tasha ne a wani shingen binciken ababan hawa da ke tsakanin Damba da Sabon Gida a garin Gusau, yayin da yake kan hanyar sa ta zuwa garinsu Mada.

Civil Defense Zamfara
Civil Defense Zamfara

“Ana zargin an same shi da tabar wiwi, da wasu haramtattun kwayoyi, da kayan soja, da suka hada da albarushi na bindiga na G3 guda uku da wani albarushi na wata bindiga AA guda Daya.” Inji Kwamandan rundunar ta Civil Defense.

Kwamanda Mustapha ya bayyana cewa, Shugaban rundunar tsaron Civil Defense na Kasa Dakta Ahmed Abubakar Audi, ya yi Allah-wadai da zargin da ake yi wa jami’in nata da aikata miyagun laifuka, kuma ya bayar da umarnin daukar matakin gaggawa akan jami'in, daga ciki har da yiwuwar korar Sarkin-Tasha daga aiki a hukumar.

Ya kuma jaddada cewa, laifin da jami’in ya aikata yayi ne a karan kan shi ba da miyon bakin hukumar ba.

Har ila yau yace a bisa alakar aiki dake tsakanin hukumomin biyu (‘Yan sanda da Civil Defense), Mustapha ya bada tabbacin cewa zai yi aiki kafada da kafada da kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara domin mika jami’in zuwa hedikwatar hukumar civil Defense ta Kasa dake Abuja domin daukar matakan ladabtarwa da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.

Ya nanata kudurin hukumar ta civil Defense na yaki da miyagun laifuka da kuma kiyaye da’a a tsakanin jami'an ta, tare da yin alkawarin tabbatar da gaskiya yayin da ake gudanar da bincike.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG