Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Yahudawa da Falasdinawa Ya Kara Tsamari a Hebron


Falasdinawa suna hushe fushinsu da jifan duwatsu da tana wuta
Falasdinawa suna hushe fushinsu da jifan duwatsu da tana wuta

Jami’an tsaron Isra’ila sun bindige Falasdinawa biyu har lahira, ciki har da daya da ya soki wani Soja da wuka.

Harin baya-bayan nan a rikicin Yahudawa da Falasdinawa da ya raba kansu a birnin Hebron da ke gabar yammacin kogin Jordan yana kara muni.

A yayin da yawan zanga-zanga da hare-hare a birnin Kudus suka lafa, fargaba ta karu a birnin Hebron, wanda hakan kusan kullum yake haifar da taho mu gamar matasa da sojojin Isra’ila.

Sojojin suna kokarin tabbatar da zaman lafiyar da ya samu fiye da shekaru 10 a birnin na gabar yammacin kogin tare da Yahudawa ‘yan share wuri zauna.

A harin wata Alhamis, wani Bafalasdine dan shekaru 23 ne ya soki wani ma’aikacin tsaron kan iyaka a kusa da bukkar da Yahudawa suka kira Cave of the Patriarchs (Patriaks) su kuma Musulmi suke kira Masallacin Sayyadina Ibrahim.

A karo na biyu kuma wani dan Bafalasdinen dan shekaru 19 ne yayi kokarin sukar sojan Isra’ila da wuka a garin na Hebron. An shafe wata daya ana rikicin.

Rikicin ya hallaka Isra’ilawa 11 da Falasdinawa 58 zuwa yanzu. Isra’ila tace yawanci Falasdinawan da aka kashe, an kashesu ne suna kokarin harbi ko sukar fararen hula ko jami’an tsaronsu.

Kwamishinan ofishin kula da ‘yancin bil’adama na MDD ya fada a ranar Laraba cewa, idan ba a maida hankali akan tsaida rikicin ba, to ya kama hanyar zama babbar masifa.

Mista Zeid Raad Al’Hussein ya dora laifin rikicin ga dukkan bangarorin biyu. Inda yace Isra’ila na amfani da karfin tuwo wajen dakile hari kan Yahudawan, su kuma Falasdinawa na bin hudubar hure kunne da shugabanninsu ke yi.

XS
SM
MD
LG