Manufar taron na kasa da kungiyar IZALA ta shirya ita ce wayar da kawunan mutane akan illar shan miyagun kawayoyi da yanzu ya addabi yawancin matasan kasar da ma wasu kasashe. An yi taron ne a garin Kontagora dake cikin jihar Neja a Najeriya
Kungiyar ta IZALA ta nuna damuwarta akan yadda tarbiyar matasa maza da mata take tabarbarewa, lamarin dake gurbata rayuwarsu, sanadiyar shan mayagun kwayoyi. Inji kungiyar IZALA shan kwaya bai tsaya kan matasan Najeriya ba kawai, har da ma wasu kasashen yammacin Afirka inda dabi'ar ke karuwa.
Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, shugaban majalisar malaman kungiyar IZALA a Najeriya ya ce matasa, maza da mata, a arewacin Najeriya suna anfani da maganin mura kwalabe fiye da miliyan daya kowace rana domin sanya wa kansu maye. Injishi, abun bakin ciki ne. Yana mai cewa dole ne a hada karfi da karfe domin a ceto al'umma.
Shi ma babban daraktan sashen agaji na kungiyar, Injiniya Imam Sitti ya ce suna hada hannu da wasu kungiyoyi domin fadakar da matasan kan illar shaye shayen. A cewarsa kwana kwanan nan suka dawo daga kasar Ivory Coast domin aikin fadakar da mutane akan illar shan miyagun kwayoyi. Ya ce suna da kyakyawar alaka da sauran kungiyoyi makamantansu da zummar kawar da dabi'ar shan miyagun kwayoyin.
Onarebul Shehu Saleh Rijjau dan majalisar wakilan Najeriya da ya halarci taron ya ce majalisarsu na dap da samar da wata doka da zata takawa masu hada hadar miyagun kawayoyi birki a Najeriya.
Ita kuwa gwamnatin jihar Neja cewa ta yi taron fadakarwar ya zo daidai lokacin da ake bukatarshi, inji mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Muhammad Ahmed Getso.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Facebook Forum