Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za’a Fara Amfani Da Sabuwar Manhajar Ilimi A Watan Janairun 2025-Minista


Ministan Ilimin Najeriya, Tahir mamman
Ministan Ilimin Najeriya, Tahir mamman

Farfesa Mamman ya bayyana cewar sabuwar manhajar zata warware matsalolin koyo da koyarwa dana samun aikin yi kasancewar sabon tsarin koyar da sana’o’in da aka kirkiro zai yi matukar tasiri wajen koyawa dalibai sana’o’in zamani.

Ma’aikatar ilmin tarayyar Najeriya ta sanar da da cewar sabuwar manhajar ilimin firamare dana karamar sakandare zasu fara aiki a fadin Najeriya a watan Janairun 2025.

Ministan Ilmin, Farfesa Tahir Mamman, wanda ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki akan yadda za’a aiwatar da sabuwar manhajar a abuja, yace za’a fara amfani da sabuwar manhajar ilmin sakandare a watan satumbar 2025.

Farfesa Mamman ya bayyana cewar sabuwar manhajar zata warware matsalolin koyo da koyarwa dana samun aikin yi kasancewar sabon tsarin koyar da sana’o’in da aka kirkiro zai yi matukar tasiri wajen koyawa dalibai sana’o’in zamani.

Ya kara da cewar za’a shafe watanni 3 masu zuwa ana sharar fage, ciki harda horas da malamai akan yadda zasu yi amfani da manhajar.

A wani labarin kuma, wani mai suna Chinaemere Opara ya maka ma’aikatar ilmin tarayyar Najeriya da hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i ta kasar (JAMB) da hukumar kula da jami’o’in kasar (NUC) a kotu a kan manufar gwamnatin dake neman takaita shekarun samun gurbin karatu a jami’o’in Najeriya.

Opara, wanda dalibin babbar sakandare ne mai shekaru 15, ya shigar da karar ne ta hannun mahaifinsa, Mr. Maxwell Opara, wanda lauya ne, a babbar kotun tarayya dake Abuja, a jiya Litinin.

Kamfanin Dillancin Najeriya (nan) ya ruwaito cewar a cikin bukatu 6 da yake neman kotu ta biya masa, mai karar ya bukaci a ayyana cewar takaita shekarun samun gurbin karatu a jami’o’in najeriya da wanda ake kara yayi nuna wariya ne kuma ya sabawa tsarin mulki.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG