Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rawar Da George Weah Ya Taka A Kwallon Kafa Kafin Zama Shugaban Kasa


George Weah da Zinedine Zidane
George Weah da Zinedine Zidane

Tsohon dan wasan kwallon kafa na kungiyar AC Milan George Weah, ya zamo zabebben shugaban kasar Laberiya, mai shekaru 51, da haihuwa kafin ya fara siyasa ya kasance shahararen dan wasan kwallon kafa a duniya inda ya fara da kungiyar kwallon kafa na matasa mai suna Young Survivors Croratown FC dake kasar laberiya, a shekarar 1981.

Ya kuma buga wasannin a manya manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya a kasashe daban daban irin su Monaco, Paris Saint-Germain, AC Milan, Chelsea, Manchester City da kuma Marseille, da sauransu.

A yayin da yake taka leda ya samu nasarar jefa kwallaye 193, a wasannin 411 da ya buga a kungiyoyi daban daban.

A wasannin da ya buga wa kasarsa ta haihuwa watau Laberiya kuwa ya zurara kwallaye 22 a wasannin 60. George Weah, ya samu lambobin yabo da dama a bangaren kwallon kafa a duniya

Inda ya taba zama Gwarzon dan wasan kwallon kafa na Duniya sau uku (African Best Player) a shekarun 1989, 1994 da 1995, ya kuma zama gwarzon dan wasan kwallon kafa na Duniya inda ya karbi kabin (Ballon'd'Or) a 1995.

Haka kuma a shekara ta 1995, ya zama gwarzon dan wasan kwallon kafa na hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA Best Player) ya kuma kasance dan wasan da yafi kowani dan wasa zurara kwallaye a raga na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai (ULC Top Scorer) 1994-95, da kuma gwarzon dan wasan Afirka na gidan Rediyon (BBC African Best Player) 1995.

Ya ajiye takalman taka ledarsa na kulob a shekara 2003 a kungiyar kwallon kafa ta Al-Jazira, Inda daga bisani ya fada siyasa a shekara ta 2015 aka zabeshi a matsayin Dan majalisar dattawa. sai kuma a 2017 da aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Laberiya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG