Mai Martaba Lamidon Adamawa, Barkindo Aliyu Mustapha ya ce rashin fitowar dattawa su tsawatarwa mabiyansu a bangarorin Najeriya, shi ke haddasa takaddamar kiraye-kirayen da ke nema ya raba kasar.
Lamido ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da wakilin Muryar Amurka, Sanusi Adamu, inda ya jaddada cewa da ana samun magabata suna fitowa suna tsawatarwa na kasa da su, da ba a tsincin kai a halin da ake ciki ba.
“Akwai Igbo wadanda sun gani sun ji, su ya kamata su yiwa matasan magana, mu ma arewa mu yiwa matasa magana, shi ke nan sai ka ga an samu zaman lafiya.” In ji Lamidon Adamawa.
Basaraken ya kuma dora alhakin fadace-fadacen da ake yawan samu a tsakanin makiyaya da manoma akan karuwar jama'a, sare gandun daji don kafa manyan masana'antu da gonaki wadanda hakan a cewars shi ke janyo karanci filayen noma da kiwo.
Ya kuma kara da cewa tashe-tashen hankula tsakanin Fulani makiyaya da manoma ya samo asali tun bayan watsi da hukumomi suka yi da tsarin rabon filayen kiwo da noma tun a 1976 da aka kirkiro kananan hukumomi a Najeriya.
“Sai suka dauki matakai na rusa burtali da gandun daji inda shanu su ke kiwo suka rabawa mutane.” In ji Lamidon Adamawa.
Saurari cikakken rahoton Sanusi Adamu domin jin cikakkiyar hirar da suka yi:
Facebook Forum