Ziyarar da Ministar Harkokin Mata, Hajiya Jummai Alhassan, ta kai hedikwatar jam’iyyar PDP a Abuja ta janyo cece-kucen siyasa, duk kuwa da cewa ba kawai tsohuwar jam’iyyarta ta PDP ta kaiwa irin wannan ziyarar ba; har ma da jam’iyyarta ta yanzu, APC, da ma hukumar zabe ta kasa (INEC).
Tuni wasu ke ganin ziyarar Ministar a hedikwatar tsohuwar jam’iyyarta a halin yanzu wata alamace cewa za ta koma, ko kuma ta na sha’awar komawa, gidanta na tsamiya. Tuni dai ‘yan PDP ke bayyana fatan cewa Ministar za ta “dawo gida.” To amma wani jigon babbar jam’iyyar adawa ta PDP kuma Sakataren Shirye-shiryenta, Sanata Abdul Ningi, ya yi nuni da cewa Ministar ta fito karara ta shaida masu cewa ba da sunan siyasa ta zo ba. Da wakilinmu a Abuja Nasiru Adamu Elhikaya ya tambaye shi ko sun dan yi zawarcinta zuwa PDP a fakaice, sai Sanata Ningi ya ce lallai sun yi wanka mai kamar jurwaye. Ma’ana sun dan gayyace.
Ningi ya jaddada cewa Ministar ‘yar PDP ce tun asali, ya ce har yanzu akwai irin darbiyyar da ta samu a tsohuwar jam’iyyarta, PDP. Sai dai Ningi ya kuma lura cewa a tawagar Ministar har da ‘yan jam’iyyar Labour Party da sauransu.
Ita dai Ministar Matan ta ziyarci PDP da APC da kuma INEC ne, saboda ta kara ankarar da mata, daga bangarori daban-daban, su ba da himma wajen shiga harkokin siyasa saboda a rika damawa da su a harkokin shugabancin Najeriya a dukkannin matakai.
Ga Nasiru Elhikaya da cikakken rahoton:
Facebook Forum