Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da sha’anin mata Dr. Amina Mohammed ta shawaraci shugabanin kasashen Afrika da su dauki matakan da za su bai wa mata da matasa damar cin gajiyar yarjejeniyar kasuwancin da suka sakawa hannu a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar.
Yayin wata hira da ta yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka a gefen taron kungiyar tarayyar Afirka, Amina ta ce, sai an kawo karshen tashe-tashen hankulan da ke addabar wasu sassan Najeriya da sauran kasashen nahiyar kafin a ci cikakkiyar gajiyar wannan yarjejeniya.
“Wannan takarda (yarjejeniya) da aka saku hannu akai, inda za a kara kasuwanci a Afirka, tana da amfani, amma ba za mu ci gaba ba idan ba mun samu mun kawo karshen wannan masifar da muke ciki ba.” Inji Amina.
A jiya Lahadi mambobin kungiyar tarayyar Afirka ta AU 54 suka rattaba hannu a birnin na Yamai a taron kungiyar karo na 33 akan yarjejeniyar kasuwancin da za ta kawar da shingayen da ke kawo tarnaki wajen cinikayya tsakanin kasashe a nahiyar.
Domin jin matakan da Amina ta ce taron ya dauka saboda ci gaban mata a nahiyar ta Afirka, saurari cikakkiyar hirar da suka yi da wakilinmu Souley Moumouni Barma: