Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Gardama Kan Cancantar Gina Jami'ar Sufuri a Daura


Batun cancantar gina Jami'ar sufuri da Gwamnatin Tarayya ke yi a Daura ta Jihar Katsina na cigaba da jan hankalin Kwararru da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi a Najeriya, ganin cewa shiyyar Arewa, da jami'ar ta ke, tana fama da matsalolin da su ka fi bukatar kulawa.

Kwararru a fannin ilimi sun nuna cewa gina irin wanan Jami'ar da za ta koya wa matasa yadda za su sarrafa ababen hawa musamman ma jiragen kasa, da yanzu ake amfani da shi, abu ne mai alfanu a kasa kuma zai ba matasa damar dogaro da kansu duk da cewa ana cikin wani yanayi na raguwar tattalin arziki. Farfesa Sani Sambo na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria yana cikin masu wanan tunanin inda ya ce a duk lokacinda aka ce Jami'a za a yi to abu ne da ya kamata yan kasa su yi na'am da ita ba wai a yi ta suka akai ba domin matasa da ke fama da rashin aikin yi za su amfana kuma a haka kasa ce za ta amfana.

To sai dai ga daya daga cikin Dattawan Arewa Dr. Usman Bugaje gina Jami'ar a Daura bai dace ba, domin a kwanan nan aka kafa wata Makarantan Kimiya da fasaha a Daura, saboda haka wanan abu bambadanci ne kawai mutane ke yi, kuma shugaban Kasa ake so a burge kuma yin haka rashin adalci ne. Bugaje ya ce sannu a hankali ma za a ce sai shugaban Kasa ne zai za6i shuwagabanin Jami'ar kuma haka zai kawo rashin jituwa.

Amma wani kwararre a fannin ilimi na bai daya, Hassan Sardauna Hammayo yana ganin yin wanan Jami'a a yanzu ya dace domin babu irin ta a kasa baki daya, kuma za a samu kwararru daga jami'ar wadanda za su habbaka fannin sufuri.

Shi kuwa mai nazari kan al'amuran yau da kullum, Abubakar Aliyu Umar ya ce ba kyauta ba ne, wannan ai cin fuska aka yi wa 'yan kasa domin za a sa mutane cikin yanayin bauta ne kawai ga kasar China. Aliyu ya ce inda Shugaba Buharin da ya sani ada ne, da ya ce kar a kai Jami'ar Daura, saboda kar a ga kamar yana da hannu a ciki.

Abubakar Aliyu ya ce an yi rashin adalci saboda jami'o'in da ake da su yanzu suna neman rugujewa saboda rashin kula. Ya ce me zai hana a habba Cibiyar Koyar da dabarun sufuri da ke Zaria idan har ana so a samu cigaba mai dorewa?

Wanan Jami'a da Kamfanin CCECC ta Kasar China ke ginawa a kyauta za ta lakume kudi har dalar Amurka miliyan 50.

Saurari cikakken bayani a rahoton Madina Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG