Daya daga cikin lauyoyin dake kare tsohon ministan Bala Muhammad, Chris Uche, SAN, ya bayyana jin dadinsa saboda a cewarsa lallai dimokradiya na aiki a kasar ta Najeriya kan hukumcin da kotun ta yanke.
Tsohon ministan na birnin Abuja ya shiga hannun hukumomi ne biyo bayan kamashin da hukumar dake yaki da cin hanci da zarmiya, wato EFCC tayi akan zargin yin almundahana da dukiyar jama'a da suka kai N864m yayinda yake gwamnati.
Lauyan nasa Chris Uche yace shigar da kara abu ne daban haka kuma tabbatar da hujja akan zargin abu ne daban.
Alkalin ya bada belin tsohon ministan bisa ka'ida ta sa hannu kan Naira miliyan dari biyar da mutane biyu masu tsaya masa cikinsu ko har da mai mukamin Sanata.
Tuhumar ba ita ba ce ta farko da hukumar EFCC take yiwa tsohon ministan ba da wasu jami'ai da dama na tsohuwar gwamnatin Shugaba Jonathan..
Ministan shari'a Abubakar Malami yace akwai wata hukuma ta musamman da zata dinga kula da dukiyoyin da aka kwato daga barayin biro. Dokar kafa hukumar har yanzu tana gaban majalisa.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum