A yanzu haka dai matsalar fyade musamman ga kananan yara, na neman zama ruwan dare a Najeriya, al'amarin da ya kai iyaye da wasu kungiyoyin kare hakkokin bil'adama, gudanar da zanga-zangar lumana a jihar Adamawa Arewa maso gabas.
Wasu iyaye da kuma 'yan fafutukar kare hakkin mata, da kananan yara ne suka yi zanga-zangar lumanar domin nuna fushinsu, na yadda ake cigaba da keta diyaucin 'ya'ya mata ta hanyar fyade, da kuma sakin wadanda ake kamawa game da zargin fyade.
Masu zanga-zangar da suka hada da iyaye mata, da maza, dama kananan yara, sun kai kukansu zuwa shelkwatar rundunar 'yan sanda, babbar kotun jihar kana da gidan gwamnati, inda suka mika kokensu.
Kungiyar lauyoyi mata ta FIDA, na cikin wadanda suka shirya wannan gangami, na nuna fushin su. Barista Halima Shuaibu Abdurrahman itace shugabar kungiyar a jihar Adamawa, ta kuma yi bayanin dalilin wannan tattakin.
Yusuf Manasa Daniel babban mai shigar da kara na jihar Adamawa na ma’aikatar Shari'a shine ya wakilci cif jojin jihar, domin bayyana matakan da zasu dauka.
Kamar yadda alkalumman hukumomin tsaro suka bayyana, a kasa da mako guda, fiye da mata kananan yara 8 ne aka yiwa fyade a jihar, banda wadanda ba’a kai rahoto ba.
Ga cikakken rahoto daga wakilin muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz.
Facebook Forum