Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce bincike ya nuna cewar ana amfani da guraben ajiya daban daban wajen sarrafa kudaden gurbatatcen man fetur na sata a kasashen waje.
Ya jaddada haka ne a hira da muryar Amurka, a birnin New York, ta kasar Amurka, a lokacin da ya ziyarci majalisar dinkin duniya.
Akan batun ‘yan matan Chibok, shugaban ya ce Gwamnati a shirye take ta saurari ‘yan kungiyar Boko Haram, idan har zasu maido da ‘yan matan da suka sace dukkan su .
Shugaba Buhari, ya tabo batun miyagun kwayoyi yana mai cewa duk wanda aka kama to lalle doka zata yi aiki ta kuma babu afuwa, ya ce Gwamnati na tattaunawa da makwabtan kasashe ta neman hanyoyin da za’a bullo wa batun.
Ya kuma umarci iyaye dasu da bayanai na duk inda sauka san ana sayarda miyagun kwayoyi da kuma sa idon akan ‘ya’yan su dan sanin irin abokan da ‘ya’yan su ke abota dasu, gyara kayan ka bai zamo sauke mu raba ba domin hannu daya baya daukar jinka.