Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Taro Kan Noma: Naira Biliyan uku Ake Kashewa Kan Abinci A Lagos Kulluyaumin


Wata gona mai yabanya
Wata gona mai yabanya

Yayin da gwamnatin Najeriya ke jaddada muhimmancin rage dogaro da man fetur da kuma komawa gona, an jaddada muhimmancin noma a wani babban taro a Lagos.

An yi wani babban taro na bunkasa fannin noma a birnin Lagos, inda jami’ai daban-daban su ka yi ta jaddada muhimmancin noma ta fannoni daban-daban. Taron, wanda gwamnatin jahar Lagos ta shirya da zummar wayar da kan jama’a kan hanyoyin bunkasa noma, da zummar rage dogaro ga man fetur da kuma ciyar da kasar gaba.

A jawabinsa, gwamnan jahar Lagos Akinwunmi Ambode ya ce kimanin Naira biliyan 3 ne jama’a ke kashewa kowace rana kan abinci a birnin Lagos. Don haka a cewar gwamnan babu hanyar samun kudin shiga da kuma fidda kai daga talauci kamar noma. Shi kuwa gwamnan jahar Kebbi Sanata Abubakar Bagudu, wanda ya jagoranci tawagar jaharsa a wurin taron, ya ce noma na da dinbin muhimmanci, kuma wannan ne ma ya sa jaharsa ta cimma yarjajjeniya da jahar Lagos kan batun noman.

Su ma sauran mahalarta taron sun yaba da wannan yinkurin. Madam Victoria Akunyumi ta ce sun baje kolin kayan gona kala-kala saboda jadda ma ‘yan Najeriya muhimmancin gomawa gona. Shi kuwa wani mai suna Hassan Alabi cewa ya yi wannan hanzarin zai sa a yada al’adar noma a Najeriya.

Ga wakilinmu Babangida Jibrin da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG